1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin yakin Yuganda ya halaka mutane

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 28, 2022

Kimanin mutane 22 ne aka tabbaatar sun rasa rayukansu, sakamakon faduwar jirgin sama mai saukar ungulu mallakar sojojin kasar Yuganda a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4HTp6
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | 'Yan Tawaye  ADF | M23
Yuganda ta tura sojojinta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango saboda 'yan tawayeHoto: Joseph Kay/AP Photo/picture alliance

Jami'in hulda da jama'a na sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ya nemi a sakaya sunansa ne ya sanar da hakan, ga kamfanin dillancin labarai na Reuters. Tun watan Disambar bara ne dai, Yugandan ta tura sojojinta zuwa makwabciyarta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, domin tallafa mata wajen yaki da 'yan tawayen da ke da alaka da kungiyar tawaye ta (ADF) ta kasar. Jami'in hulda da jama'a na rundunar sojojin Yugandan UPPDF Felix Kulayigye ya tabbatar da faduwar jirgin mai saukar ungulu mallakar rundunar, sai dai bai yi wani karin haske ba.