Mutane fiye da 80 sun mutu a hare-hare a Ankara | Labarai | DW | 10.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane fiye da 80 sun mutu a hare-hare a Ankara

Gabanin gangami adawa da tashe-tashen hankula ne bama-bamai biyu suka tashi a tashar jirgin kasa na Ankara babban birnin Turkiya inda mutane 80 suka rasu.

Wasu tagwayen hare-hare da suka wakana a gaban tashar jirgin kasa ta Ankara babban birnin Turkiya sun hallaka mutane akalla 80 tare da jikata wasu karin mutane 120. Bama-bamai biyu ne suka tarwatse a lokacin da jama'a suka fara taruwa da nufin gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da tashe-tashen hankula da ke wakana a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wannan ta'asar. Sai dai kuma gwamnatin Turkiya ta na kokarin tantance ko 'yan kunar bakin wake ne suka aiwatar da su. Firaministan wannan kasa Ahmed Davutoglu ya na gudanar da taron kwamitinsa na tsaro na gaggawa don daukan matakan da suka dace.

Turkiya dai ta samu kanta cikin wani sabon rikici aware na kurdawa, a daidai lokacin da ya rage makonni uku a gudanar da zaben 'yan majalisa.