Mutane da dama sun salwanta a Kwango
May 27, 2019Talla
Akalla mutane 30 ne suka mutu yayin da wasu kimanin 200 kuwa suka bata a Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango, sakamakon nitsewar da wani jirgin ruwa ya yi.
Lamarin ya faru ne a tafkin Mai-Ndombe da ke a yammacin kasar, a daren Asabar da ya gabata.
Al'umar Kwangon dai sun fi amfani ne da sufurin ruwa, abin kuma da ya sanya yawaitar hadarin na ruwa a kasar.
Ana kuma danganta hakan da yawan daukar mutane da kayayyaki fiye da kima.
Kwararru sun ce daga cikin dalilan da ke sanya samun asarar rayuka a galibin haduran, sun hada ne da rashin amfani da rigunan kariya da kuma rashin kwarewa a harkar iyo.
Ko a watan jiya ma, an yi asarar rayukan mutum 167 a wasu haduran biyu dabam-dabam.