Mutane da dama sun mutu a Somaliya | Labarai | DW | 31.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun mutu a Somaliya

Jamia'ai a Somaliya sun ce mutane 25 ne suka salwantarsu bayan wata arangama tsakanin mayakan Al Shabaab da dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Akalla mutane 25 ne jami'ai suka tabbatar da salwantarsu a Somaliya bayan wata arangama tsakanin mayakan Al Shabaab da dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka ta AU. Lamarin dai ya faru ne a yankin Shabelle kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Mayakan Al Shabaab, sun yi ikirarin halaka dakarun na AU 39 a kwanton baunar da suka yi wa sojojin, sai dai har ya zuwa yanzu ba su tabbatar da sahihancin ikirarin ba. Rahotanni sun ce mayakan na tawaye na tsananta hare-hare kan dakarun na kasashen na Afirka.

Kimanin dakaru dubu 20 ne dai kungiyar ta AU ta girke a Somaliyar musamman saboda fuskantar 'yan jihadin na Al Shabaab.