Mutane da dama sun mutu a hari a Turkiya | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun mutu a hari a Turkiya

Harin ya wakana a birnin Suruc da ke a kudancin kasar kusa da birnin Kobane na kasar Siriya inda mutane kimanin 30 suka mutu yayi da wasu kusan dari suka ji rauni.

A kasar Turkiya mutane kimanin 30 sun hallaka a yayin da wasu kusan dari suka ji rauni a cikin wani harin ta'addanci da aka kai a birnin Suruc da ke a kudancin kasar. Hukumomin kasar sun tabbatar da afkuwar lamarin wanda suka ce ya wakana ne a harabar cibiyar raya al'adu ta birnin wanda ke kusa da birnin Kobane na kasar Siriya inda mayakan kurdawa suka kori mayakan kungiyar IS a cikin watan Janairu.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, kuma su ma hukumomin kasar ba su kai ga dora alhakin kai shi ba ga wata kungiya ba. Sai dai tuni aka soma zargin kungiyar IS da kai wannan hari wanda idan hakan ta tabbata to kuwa wannan shi ne harin ta'addanci na farko da kasar ta Turkiya ta fuskanta tun bayan bulluwar kungiyar ta IS a duniyar larabawa