Mutane da dama sun hallaka a harin Manchester | Labarai | DW | 23.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun hallaka a harin Manchester

Rahotanni daga Birtaniya na cewa akalla mutane 22 ne suka mutu yayin da sama da 50 kuma suka jikkata bayan tashin wasu nakiyoyi cikin daren Litinin a wani gida na raye-rayen nan na Manchester Arena.

Bayanai sun ce fashewar da 'yan sanda ke ganin ta yiwu hari ne na ta'addanci ta faru ne da misalin karfe 10:30 agogon GMT a dai dai lokacin da wata mawakiya 'yar Amirka, Ariana Grande ke kammala wani wasa da ta yi a gidan rawan. Mawakiyar dai ta ce babu wani abin da ya same ta a harin. Faraiministar Birtaniya Theresa May ta yi Allah wadai da harin da ta ce ya matukar tayar da hankali kuma ma tuni ta ce ta dakatar da yakin neman zaben ta ke yi.

Tuni dai kasashen duniya ciki har da Jamus suka aikewa Burtaniya din sako na taya jaje kan abinda ya faru. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce sun kadu da jin wannan labari kuma suna yi wa al'ummar Burtaniya din ta'aziyya da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Yanzu haka dai kwararru a fannin kwance bama-bamai da sauran jami'an 'yan sanda a birnin na can suna ta sintiri a birnin.