1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane biyar sun mutu cikin wani hari a Kamaru

Gazali Abdou tasawaSeptember 20, 2015

Wasu yara ne biyu suka kai harin ƙunar bakin waken a garin Mora na yankin arewacin ƙasar ta Kamaru kusa da kan iyaka da Najeriya.

https://p.dw.com/p/1GZOB
Kamerun Anschlag in Maroua
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Hukumomin sojin ƙasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane biyar da suka haɗa da ɗan sanda guda a cikin wasu tagwayen hare-haren da wasu 'yan ƙunar baƙin wake suka kai da sanhin safiyar wannan Lahadi a unguwar Galdi ta birnin Mora na yankin arewacin ƙasar kusa da kan iyaka da Najeriya.Hukumomin tsaron ƙasar ta Kamaru sun ce wasu ƙananan yara ne dai macce da namiji suka kai wannan hari inda suka tayar da bam ɗin da ke jikinsu a lokacin da wani ɗan sanda ya nemi ya bincikesu a kan hanyarsu ta shiga birnin na Mora wanda kasuwarsa ke ci ranar Lahadin nan inda dubban jama'a suka taru domin sayen raguna Sallahlayya.

Hukumomin sojin ƙasar ta Kamaru sun ce tuni suka aika da masu bincike a gurin da aka kai harin a yayin da a share daya jami'an tsaro suka shiga farautar wasu mutanen ukku da ke tare da masu ƙunar bakin waken, da suka tsere bayan abkuwar lamarin.