Mutane a Kenya na zaben Shugaban kasa | Siyasa | DW | 07.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mutane a Kenya na zaben Shugaban kasa

Al'umar kasar Kenya sun yi fitowar dango domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da babban mai kalubalantarsa Madugun adawa Raila Odinga.

Jama'a a Kenya sun yi fitowar dango domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da babban mai kalubalantarsa Madugun adawa Raila Odinga. Ana sa ran fitowar jama'a sosai duk da fargabar da wasu ke baiyanawa ta yiwuwar tashin hankali. Mutane kimanin miliyan ashirin ne ake sa ran za su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar dana majalisun dokoki da kananan hukumomi.

Yan takara takwas ne dai ke fafatawa domin neman kujerar shugabancin kasar, amma takarar ta fi zafi ne tsakanin jiga jigan yan siyasa biyu shugaba mai ci Uhuru Kenyatta mai shekaru 55 da kuma madugun adawa Raila Odinga mai shekaru 72.

Yan takarar biyu dai 'ya'ya ne ga mutanen da suka yi gwagwarmayar kwatowa kasar ta gabashin Afirka yancin kai daga turawan mulkin mallaka. Suna fafatawa a karo na biyu a zaben da masharhanta ke cewa za'a yi kan kan kan.

Tun da sanyin safiya mutane suka yi jerin gwano a rufunan zabe da aka bude da misalin karfe shida na safe.

Shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati ya baiyana gamsuwa da yadda jama'a suka fito domin kada kuri'a duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya kawo jinkiri a wasu yankunan.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da fiye da masu kada kuri'a dari biyu a yankin da 'yan adawa suka fi karfi na Kisumu suka gudanar da zaman dirshin a ofishin hukumar zaben suna masu ikirarin babu sunayensu a rigistar masu zabe. Tuni a ka fara raba kayayyakin zabe daga shalkwatar zabe da ke Nairobi karkashin tsauraran matakan tsaro. An kuma jibge 'yan sanda 150,000 don sa ido a zaben. Tsohon sakataran harkokin wajen Amirka John kerry da tsohuwar Firaministan kasar Senegal AminataToure sun gana da jami'an hukumar zaben kasar inda su ka bayyana gamsuwar su da shirye-shiryen zaben. 

Sauti da bidiyo akan labarin