Mutane 80 sun hallaka cikin harin Pakistan | Labarai | DW | 17.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 80 sun hallaka cikin harin Pakistan

Yawan mutanen da harin bam na Pakistan ya hallaka sun haura 80, yayin da wasu 180 su ka samu raunuka

Yawan mutanen da harin bam na Pakistan ya hallaka sun haura 80, yayin da wasu 180 su ka samu raunuka, kamar yadda jami'ai su ka tabbatar.

An kai harin cikin wata kasuwa mai shake da jama'a a garin da ke da akasarin mabiya Musulmai 'yan Shi'a, wadanda su ne tsirarru a kasar. Tuni wata kungiya ta dauki alhakin kai harin.

Ana yawaita kai hare hare kan birnin na Quetta, kuma a wannan harin na karshen mako, tamkar ruwa ce mai cike da ababen fashewa ta tarwatse.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh