1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 49 sun mutu a fada a Afghanistan

Mouhamadou Awal Balarabe
September 17, 2020

Karawar da aka yi tsakanin dakarun gwamnatin Afghanistan da 'yan Taliban ta salwantar da rayukan mutane da yawa, a yayin da ake gudanar da tattaunawar samar da zaman tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3idk9
Afghanistan Tora Bora Soldaten
Hoto: Imago/Xinhua/R. Safi

Kazamin fada tsakanin sojojin Afghanistan da 'yan Taliban ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a gabashin kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu. Mai magana da yawun gwamnan lardin Nangarhar, Ataullah Khogyani ya ce an kashe dakarun gwamnati 20, yayin da  mayakan Taliban 29 suka kwanta dama, 20 kuma suka jikkata. Ya zuwa yanzu dai maharan ba su mayar da martani a hukumance a kan abin da ya faru ba.

Wannan fadan na zuwa ne yayin da gwamnatin Afghanistan da 'yan Taliban suka fara musayyar yawu tsakaninsu a Doha, da nufin kawo karshen rikicin da ya addabi kasar tun daga 2001. Yawancin manyan jami'an Afghanistan sun yi kira da a tsagaita wuta, amma har yanzu kungiyar Taliban ba ta ce uffan a kan wannan bukatar ba.

An samu tsaiko na watanni kafin a fara tattaunawar sulhu a ranar Asabar sakamakon sakarkakiya da aka samu kan musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu.