1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 40 sun mutu a Mali

April 29, 2018

Akalla mutane 40 sun mutu a kashe-kashen da 'yan bindiga masu kaifin kishin addini suka kaddamar a kan iyakar Mali da Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/2wrTd
Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Hukumomi a kasar Mali, sun ce akalla mutane 40 sun mutu cikin makonni biyun da suka gabata, a kashe-kashen da 'yan bindiga masu kaifin kishin addini suka kaddamar a kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar. Gwamnan yankin Menaka Daouda Maiga, ya ce a ranakun Alhamis da Juma'a da suka gabata ma sai da wasu 'yan bindiga bisa babura suka buda wuta kan jama'a.

Ya kuma yi zargin wasu makiyaya da ke alaka da kungiyar IS a yankin da kaddamar da hare-haren a matsayin ramuwar gayya kan sojojin yankin. Ana dai ganin karin hare-hare a tsakanin kasashen na Mali da Nijar a 'yan tsakanin nan a yankin arewa maso gabashin kasar. Hare-haren dai na iya zama wani yunkuri ne na ta'azzara lamura tsakanin Fulani da kabilun yankin, kan ikon mallakar filaye.