Mutane 26 sun mutu a harin Texas | Labarai | DW | 06.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 26 sun mutu a harin Texas

Dan bindiga ya buda wuta kan mutane a wata majami'a da ke jihar Texas na Amirka, inda ya halaka mutane 26 ciki har da kananan yara.

Wani dan bindiga ya buda wuta kan masu ibada a wata majami'a da ke Sutherland Springs a jihar Texas na Amirka a jiya Lahadi, inda ya halaka mutane 26 ciki har da wata mata mai dauke juna biyu da kuma kananan yara.

Gwamnan jihar ta Texas Greg Abbott, ya ce wannan harin wanda ya kuma jikkata wasu akalla 20, shi ne hari mafi muni da jihar ta gani a tarihi. Mr. Abbott ya bayyana matukar takaice faruwar lamarin a wajen ibada, yana mai mika alhinin gwamnati ga iyalan wadanda harin ya shafa.

Hukumomin yankin dai ba su bayyana maharin ba, sai dai wasu jami'ai ciki har da na tsaro, sun ce sunan da bindigar, Devin Kelly. Shi dai Kelly, wanda rahotanni suka ce shi ma an sami gawarsa cikin motar da ya ke tukawa tare da wasu tarin makamai, mazaunin San Antonio ne. Ba a dai danganta harin da kungiyoyin masu ta'addanci ba.