1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta kashe fiye da mutane 60,000 a duniya

April 5, 2020

A duniya gaba daya kawo yammacin Asabar din akwai mutane sama da 1,100,000 da suka kamu da annobar Coronavirus, 60,000 daga cikin wannan adadi sun mutu yayin da 242,100 suka warke daga cutar. 

https://p.dw.com/p/3aSvU
Chile Huara | Coronavirus | Menschen aus Bolivien
Hoto: Getty Images/AFP/I. Munoz

A cikin jerin kasashe 200 da aka samu bullar cutar a duniya, kasar Amirka ita ce tafi masu dauke da cutar inda yanzu haka kasar ke da mutum 276,000. Kasar Italiya kuwa ita ce cutar tafi kashe mutane inda mutane sama da 14,000 suka salwanta a sakamakon Coronavirus. Jamus na da mutane sama da 90,000 da suka kamu, sai dai cutar ba ta kisa sosai a Jamus kamar yadda take yi a Spain da Italiya da Faransa da Birtaniya.