Mutane 24 suka rasu a zanga-zangar Burkina Faso | Labarai | DW | 26.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 24 suka rasu a zanga-zangar Burkina Faso

Kwamitin da ya tattara bayanai kan irin asarar da ta biyo bayan zanga-zangar Burkina Faso da ta yi awon gaba da gwamnatin Blaise Compaore ya mika rahotonsa.

Masu zanga-zangar da suka fusata da tsawon wa'adin mulkin Blaise Compaore da ya nemi a kara masa wa'adin mulki bayan kusan shekaru 30 yana dare bisa kan mulki sun sanya wuta a majalisar dokokin kasar da ma tilastawa tsohon shugaban sauka daga kujerar sa a ranar 31 ga watan Oktoba da ta gabata.

Clarisse Ouoba, da ta jagoranci kwamitin ta bayyana wa manema labarai cewa mutane 24 ne suka rasu a lokacin zanga-zangar a yayin da wasu sama da dari shida suka samu raunika sannan an afkawa gidajen wasu ministoci da 'yan majalisa inda aka yi musu sace-sace. ko da ya ke tun da fari 'yan adawa sun ce mutane talatin ne suka rasu a rikicin.

Yanzu dai gwamnatin rikon kwarya ke jan ragamar mulkin wannan kasa da ke a yammacin Afrika a inda ake saran gudanar da zabe a shekara me zuwa.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu