Mutane 18 sun mutu a harin Ouagadougou | Labarai | DW | 14.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 18 sun mutu a harin Ouagadougou

A Burkina Faso wasu da ake zargin mayakan jihadi ne sun kashe mutane akalla 18 a wani hari da suka kai a wani gidan sayar da abincin Turkawa da ke Ouagadougou babban birnin kasar.

A kasar Burkina Faso wasu da ake zargin mayakan jihadi ne sun kashe mutane akalla goma sha bakwai a wani hari da suka kai a wani gidan cin abinci na Turkawa da ke Ouagadougou babban birnin kasar, al'amarin ya auku ne a daren jiya Lahadi a gidan cin abincin na Turkawa inda akasari baki ke yawan zuwa. A halin da ake ciki dai jami'an tsaron kasar sun ce sun halaka uku daga cikin maharan a musayar wuta a tsakaninsu da maharan, sai dai akwai wasu mutane da ba a san adadinsu ba da maharan ke ci gaba da yin garkuwa da su a cikin ginin da aka kai harin.

Ministan yada labaran kasar Remi Dandjinou ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin tare da cewa akwai wasu mutane fiye da tara da suka sami rauni baya ga mutane goma sha bakwai da suka rasa rayukansu, ya kuma ce mamatan baki ne yawancinsu daga kasashen waje, Rahotanni a kasar na cewa akwai Bafaranshe guda a cikin wadanda suka mutu. Wannan shi ne hari mafi muni da aka kai a kasar bayan wanda aka kai a shekarar ta 2016 da ya halaka mutane 30. Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.