Mutane 120 suka mutu a Yemen | Labarai | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 120 suka mutu a Yemen

Rikici mai nasaba da addini a tsakanin 'yan sunni da 'yan shi'a a Yemen, na neman sauya salon rikicin da ya addabi kasar , wacce a baya ta sha fama da al-Qaida.

Fada tsakanin bangarori biyu masu adawa da juna na 'yan sunni da Shia a titunan biranen kasar Yemen a rana ta biyu Juma'a, ya yi sanadin kisan akalla mutane 120, dubbai kuma suka kaurace wa muhallansu da ma yunkurin kusan rufe babban filin tashi da saukar jiragen saman kasar.

Wannan fada dai na neman zama wani babban kalubale da ke sanya fargabar ci gaban samun wani mummunan rikici mai nasaba da addini da ba a ganshiba a wannan kasa cikin shekaru gwammai.

Babban rikicin da ke damun wanan kasa dai bai wuce fada tsakanin dakarun gwamnati da mambobin kungiyar al-Qaida ba, wacce ke gudanar a ayyukan ta a yankun kudancin kasar mai yawan tsaunika, se dai yanzu rikicin kasar na neman sauya salo bayan da mayakan aware na 'yan shia Hawsiyin a watannin baya-bayannan ke neman zama babbar kungiya da ayyukan ta ke kara fadada a arewacin kasar, ta ke kuma kama birane dama yin fada a babban birnin kasar Sana'a.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo