Mutane 12 sun mutu a wani hari a Kabul. | Labarai | DW | 25.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 12 sun mutu a wani hari a Kabul.

Wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin kai hari hukumar leken asiri ta Afghanistan a Kabul, harin da kungiyar IS ta ce ita ce ta kitsa shi.

Mutane goma sha biyu da suka hada da fararen hula da jami'an tsaron Afghanistan sun rasa rayukansu a wasu hare hare mabanbanta a Kabul da kuma lardin Helmand a kudancin Afghanistan. Wani yaro dan kunar bakin wake dan kungiyar IS ya hallaka mutane shida bayan da ya tarwatsa kansa a kusa da ofishin hukumar leken asiri a Kabul da bam din da yake dauke da shi a cewar Nasrat Rahimi mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ta Afghanistan. Jami'an tsaro biyu na daga cikin wadanda suka rasu. Wasu mutane bakwai kuma sun jikkata. Kungiyar Is ta baiyana cewa ita ce ta kai hari. A cewar kungiyar dan kunar bakin waken ya sami nasarar kaiwa ga babbar kofar shiga ofishin hukumar leken asirin inda ya tada nakiyar ya kluma hallaka mutane 30.