Musulmin Rohingya sun shige Bangaladash
August 28, 2017Talla
Rahotanni daga Bangaladash, na cewar musulmi 'yan kabilar Rohinga kimanin dubu guda suka kutsa ta karfin tsiya, suka kuma shige cikin kasar a wannan Litinin. 'Yan kabilar dai sun yi zaman kwanaki biyu a kan iyakar kasar ta Bangaladash, bayan guje wa rigima da 'yan Budha da ke a kasar Bama. Bayanai sun ce daruruwan mutanen sun fuskanci fushin dakarun kasar ta Bama ne, lokacin da wasu suka far wa shingen binciken jami'an tsaro a yammacin kasar a karshen mako. Dakarun sun ce 'yan kabilar ta Rohinga sun arce ne lokacin da suka ji aman harbe-harben da dakarun kasar Baman suka sako, yayin da suke iyakar kasar. Yanzu dai 'yan Rohingya dubu tara ne ke a cikin Bangaladesh tun da rigima ta barke tsakaninsu da 'yan tawayen kasar Bama.