Musharraf na cikin daurin talala | Labarai | DW | 19.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musharraf na cikin daurin talala

'Yan sanda sun gurfanar da tsohon Shugaban Pakistan Pervez Musharraf a gaban kotu, kafin daga bisani a mayar da shi gida domin shan daurin talala.

'Yan sanda sun cafke tsohon Shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf a gidansa da ke wajen Islamabad babban birnin kasar da sanyin safiyar wannan Jumma'a, inda aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhuma na wasu abubuwan da ya aikata lokacin da ya ke rike da madafun iko. Daga bisani tsohon Shugaban ya koma gida, inda zai ci gaba da zama karkashin daurin talala. A wannan Alhamis da ta gabata kotu ta ba da umurnin cafke tsohon shugaban Musharraf, amma masu kare lafiyarsa suka fice da shi daga kotun zuwa gida.

Tuni lauyoyinsa suka ce za su nemi kotun kolin kasar ta yi fatali da umurnin na daurin talala. Pervez Musharraf tsohon Janar na soja, ya mulki kasar ta Pakistan na tsawon shekaru tara, daga shekara ta 1999 zuwa 2008. Yanzu haka an yi watsi da takardun takaransa yayin zaben kasa baki daya da ke tafe.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe