Musayar miyau a babban zauren Mdd | Siyasa | DW | 18.07.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Musayar miyau a babban zauren Mdd

Kasashe daban daban na wasu nahiyoyi a duniya naci gaba da gararanbar neman kyakkyawan wakilci a Mdd

default

Ya zuwa yanzu dai rahotanni da suka iso mana na nuni da cewa ministocin harkokin waje na kasashen nan na G4, wato Jamus da India da Japan da kuma Brazil a hannu daya kuma da tawagar kungiyyar hadin kann kasashen Afrika wato Au sun gaza cimma matsaya guda game da bukatun da bangarorin biyu suka mika na yiwa Mdd Garanbawul din.

Wadannan daftari guda biyu da aka mika bayanai sun nunar da cewa suna kamanni da juna to sai dai inda suka sha ban ban da juna, shine na cewar, Daftarin kasashen nan na G4, bai bukaci sabbin kasashen da za a sa a cikin jerin mambobi masu zaunanniyar kujera su samu iko na hawa kujwerar naki ba kamar tsoffin mambobin ba.

To amma daftarin da kungiyyar Au ta mika ya bukaci sabbin kasashen da zasu samu shiga wannan zaure su sami cikakken iko irin na tsoffin mambobin dake kwamitin sulhu na Mdd.

Duk da cewa an fuskanci wannan hali a lokacin wannan ganawa, ministan harkokin wajen kasar India wato Natwar Singh cewa yayi tattaunawa tayi armashi kwarai da gaske.

A dai lokacin wannan tattaunawa a tsakanin bangarorin biyu data wakana a birnin New york na Amurka a jiya lahadi, rahotanni sun shaidar da cewa sun mayar da hankali ne wajen tattauna matakan yiwa Mdd garanbawul kamar yadda a can baya dukkannin su suka bukaci a aiwatar da hakan.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni da suka iso mana na nuni da cewa a ranar 25 ga watan nan da muke ciki ne aka shirya komawa teburin sulhu a can birnin Geneva, a tsakanin ministocin harkokin wajen na kasashen G4 da kuma tawagar kungiyyar Au don cimma matsaya guda, bisa manufar dogaro da magana daya don ko kwalliya ta biya kudin sabulu bisa manufar da aka sa a gaba.

 • Kwanan wata 18.07.2005
 • Mawallafi ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvao
 • Kwanan wata 18.07.2005
 • Mawallafi ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvao