Mummunan harin kunar bakin wake a kudancin Somaliya | Labarai | DW | 22.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mummunan harin kunar bakin wake a kudancin Somaliya

Wani harin kunar bakin wake da aka dora alhakinsa ga kungiyar Al-Shabbab ya hallaka sojoji a kalla 14 tare kuma da jikkata wasu a kalla 20 a kudancin Somaliya.

Harin dai ya wakana ne a cikin wani gina na Jami'a da ke kauyen birnin Kismayo, inda dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Kenya na AMISOM da ke karkashin inuwar Tarayyar Afirka da kuma na kasar ta Somaliya suke. Wata karamar sapa ce dai shake da bama-bamai ta tarwatse a sashen motsa jiki na sojojin inda nan take sojoji 14 suka rasu tare da jikkata a kalla 20 a cewar Mohamed Abisalad, jagoran sojojin na Somaliya a birnin Kismayo, sannan kuma shaidun a babban asibitin birnin sun tabbatar da wannan adadi.