Muhawarar manyan ′yan takarar zaben EU | Labarai | DW | 15.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Muhawarar manyan 'yan takarar zaben EU

Manyan 'yan takara a zaben Kungiyar EU na shirin fafatawa a muhawarar talabijin da ke zama ta karshe kafin miliyoyin al'umma a kungiyar su kada kuri'ar zaben da ke zama mafi girma ranar 23 zuwa 26 ga Mayu.

Belgein Brüssel Conflict Zone Debate (DW/M. Martin)

Muhawarar "Conflict Zone Debate" a birnin Brussels kan ina EU ta dosa

Za a yi muhawara ta wannan rana ta Laraba tsakanin manyan 'yan takara shida da ke neman kujerar Jean-Claude Juncker shugaban Hukumar Tarayyar Turai, babbar hukuma da ke lura da sha'anin gabatar da dokoki na EU da kuma ke bibiya don tabbatar da ganin an mutunta dokokin.

Babu dai 'yan Turai sai 'ya'yanta ko masu kin baki a muhawarar da za a yi karfe bakwai agogon GMT duk da cewa ana sa rai za su taka rawa sosai a zaben musamman a Birtaniya da Faransa da Italiya. Kimanin mutane miliyan 400 suka cacanci su kada kuri'a a zaben na 'yan majalisar Tarayyar Turai ko da yake a lokuta da dama masu zaben ba su cika yawa ba idan aka duba yawan wadanda suke da damar yin zaben.