Muhawara kan zaben Amirka | Labarai | DW | 05.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Muhawara kan zaben Amirka

'Yan takaran mataimakin shugaban Amirka sun yi muhawara kan yadda za su tafiyar da harkokin mulkin kasar.

'Yan takaran mataimakin shugaban Amirka sun yi muhawara ta farko kana ta karshe, inda mutanen biyu suka facaccaki juna. Tim Kaine na jam'iyyar Democrat wanda yake mara wa Hillary Clinton baya, ya kalubalanci Mike Pence na jam'iyyar Republican, wanda yake mara baya wa Donald Trump kan batutuwa da dama, da suka hada da masu sarkakiya. Sai dai anasa bangaren Mike Pence na jam'iyyar Republican a tsanake ya mayar da martani tare da kare manufofin da suka saka a gaba.

Mutanen biyu sun fafata tsawon mintoci 90, kuma ita ce muhawara guda daya tilo da aka tsara kan wadanda suke takaran mataimakin shugaban kasa.