1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Zimbabwe

August 3, 2013

Duk da zarge-zargen tabka maguɗi da kura-kuran da ake ƙorafin an samu a tsarin gudanar da zaɓen na Zimbabwe, Hukumar Zaɓen ƙasar ta tabbatar da Mugabe a matsayin zakara

https://p.dw.com/p/19JP9
Zimbabwe's President Robert Mugabe addresses a media conference at State house in Harare, on the eve of the country's general elections, July 30, 2013. Heavily armed riot police deployed in potential election flashpoints in Zimbabwe on Tuesday on the eve of a poll showdown between Mugabe and Prime Minister Morgan Tsvangirai that remains too close to call. REUTERS/Philimon Bulawayo (ZIMBABWE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Robert Gabriel MugabeHoto: Reuters

Shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi nasarar samun damar yin tazarce kan kujerar shugabancin ƙasar a karo na bakwai, Shugabar hukumar zaɓen ƙasar Rita Makarau ce ta bayar da wannan sanarwar a hukumance da wannan yammacin.

"Mugabe Robert Gabriel na jamiyyar ZANU PF shi ne aka tabbatar a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar jamhuriyar Zimbabwe daga yau uku ga watan Ogostan shekarar 2013"

Alƙaluman dai sun nuna cewa Mugabe mai shekaru 89 ya sami kashi 61 da digo tara cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa a yayin da jamiyyar Frime Minista Morgan Tsvangirai ta zo na biyu da kashi 33 da ɗigo tara cikin 100.

Tuni dai Tsvangirai ya ce zaɓukan na shugaban ƙasa da na 'yan Majalisa ba halatattu ba ne, inda ya yi zargin magudi ya kuma yi gargadin cewa ƙasar na gab da faɗawa cikin rikici na siyasa, kuma ya jaddada cewa zai kai ƙara Kotu ya kuma gabatar da ƙorafinsa a gaban ƙungiyar Tarayyar Afirka AU da ta raya tattalin arziƙin ƙasahsen Kudancin Afirkan wato SADC.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar