1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan cirani 10 sun mutu a kokarin shiga Turai

Ramatu Garba Baba
November 17, 2021

Gawarwakin 'yan cirani kimanin 10 aka gano a cikin wani jirgin ruwa da ke kokarin shiga da su nahiyar Turai ta barauniyar hanya daga kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/436fE
Italien | Sea-Watch 3 Rettungseinsätze vor der libyschen Küste
Hoto: ROPI/picture alliance

An gano gawarwakin 'yan ciranin a cikin wani karamin jirgin ruwan da ke kokarin jigilarsu zuwa Nahiyar Turai ta barauniyar hanya. Sun gamu da ajalinsu ne a sakamakon cunkoso a cikin jirgin da aka ce, ya dauko mutane fiye da kima.

Rahotanni na cewa,  jirgin da ya taso daga gabar ruwan Libiya, ya kwashi fiye da sa'oi 13 yana jiran samun damar tsallakawa da su zuwa Turai. Yan cirani akalla dari da tamanin da shida ne jirgin ya kwaso ciki har da dan watanni goma da haihuwa.

Wata tawagar Kungiyar Likitoci mara shinge ko Doctors Without Borders da ta kai agaji bayan jin koken sauran fasinjojin, ta baiyana kaduwa da kuma damuwarta kan yadda rayuka ke salwanta a tekun Mediterranean a kai-akai.