Mozambik na ci gaba da samun tallafi
March 31, 2019Talla
Kasar China ta aika da kwararrun likitoci birnin na Beira, yayin da wasu masu aikin agaji suka yi ta feshin magungunan yaki da cutar kwalara a ranar Lahadi.
Jami'ai sun ce sama da mutum 270 ne cutar ta kama, koda yake babu rahoton rasa rai da aka ji kawo yanzu.
Sama da mutum 500 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hukumance, sakamakon guguwar mai suna Idai da ta afka wa yankin makonni biyun da suka gabata. Wasu 250 ma sun mutu a kasashen Zimbabuwe da Malawi.
Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO, ta ce a gobe Litinin za a sami alluran rika-kafin cutar akalla dubu 900.