Mouhamadou Issoufou ya yi jagorancin Jamhuriyar Nijar daga 2011 zuwa 2016 karkashin jam'iyyar PNDS Tarayya.
A shekara ta 2016 ne aka sake zabarsa wani sabon wa'adin a matsayin shugaban kasa karkashin jam'iyyar tasa ta PNDS, zaben da 'yan adawa suka ce ba su amince da shi ba.