Habaka dangantakar Jamhuriyar Nijar da Amirka | Siyasa | DW | 09.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Habaka dangantakar Jamhuriyar Nijar da Amirka

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana samun tallafi daga Amirka musamman kan fannin tsaro inda suka sake duba yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.

Ibrahim Yacouba Außenminister Niger

Ibrahim Yacouba Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ce hadin gwiwa da ta Amirka sun yi wani taro na wuni daya da zummar duba halin da huldar kasashen ta ke ciki ta fannin tsaro. Nijar na daga cikin wasu kasashe 6 na Afirka da ke cin moriyar wani shiri da Amirka ta ke da shi ga kasashen don inganta tsaro abubuwan da suka ba ta damar kafa sansanonin soja da girke makamai a yunkurin Amirka na yaki da ta’addanci.

Jamhuriyar ta Nijar tana samun gajiya gami da fannin tsaro da wasu fannoni masu muhimmanci daga Amirka.

Sauti da bidiyo akan labarin