Moscow: Ba abinda ya shafemu da makomar siyasar Navalny | Labarai | DW | 20.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Moscow: Ba abinda ya shafemu da makomar siyasar Navalny

Fadar gwamnatin Kremlin ta ce ba abinda ya shefeta da makomar siyasar madugun adawar kasar Alaxy Navalny da ke tsare.

Gwamnatin Moscow ta fadi haka ne a yau bayan da Navalnin ya rasa nasara a kotu kan ikirarin cewa tsare shi da aka yi na tsawon shekarui uku na da nasaba da karya lagon siyasarsa dukd a cewa kotun ta rage wa'adin zamansa a kurkuku zuwa shekaru biyu da rabi.

Tun dai ba yau ba ana ganin Alaxy Navalny a mastayin kalubale ga shugabancin Vladimir Putin, matakin da ya kai zargin gwamnati da hannu a shayar da madugun adawar gubar da ya tsira dakyar. Sai dai duk da nesanta kai da zargin, gwamnatin ta sake tsare Navalni a ranar da ya dawo jinya daga Jamus.