Moden Lumana Afirka jam'iyya ce da ke cikin jerin jam'iyoyin da ake da su a jamhuriyar Nijar kuma ta na daga cikin jam'iyyun da suka yi fice a kasar.
A cikin shekarar 2016 jam'iyyar ta yi takara da jam'iyyar PNDS da ke mulki domin samun shugabancin kasar sai dai ba ta yi nasara ba. A wannan lokaci jam'iyyar ta Moden Lumana ita ce mafi girma a wani gungun jam'iyyun adawa da aka yi mai suna COPA.