1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

MMD za ta yi zama a kan rikicin kasar Habasha

November 5, 2021

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya shirya wani zama domin nazarin halin da ake ciki game da rikicin kasar Ethiopia da mayaka masu neman 'yancin yankin Tigray.

https://p.dw.com/p/42c2C
USA | UN-Sicherheitsrat zu Äthiopien
Hoto: Loey Felipe/UN Photo/Xinhua/picture alliance

Zaman da kasar Mexico ta bukaci a yi shi, ana sa ran mambobin kwamitinin na sulhu 15 za su halarta. Bayanai na cewa za a bude wani bangare na taro, yayin kuma da daya zai kasance na keke-da-keke.

Jami'an diflomasiyya sun ce kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsara fid da sanarwar hadin gwiwa, sai dai Rasha ta bukaci da a jinkirta hakan, a ranar Alhamis.

Da yammacin Alhamis din ne kuma ofishin jakandancin Amirka da ke Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia, ya bai wa jami'ansa damar iya ficewa daga kasar idan har suka zabi hakan.

Ofishin na ganin rikicin na Ethiopia na iya kawo nakasu ga aikace-aikacensa da ma lafiyar ma'aiktan.