1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan tsaron Isra'ila ya yi murabus

Gazali Abdou Tasawa
November 14, 2018

Ministan tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman ya yi murabus domin nuna rashin amincewarsa da matakin Firaminista Benjamin Netanyahu na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas.

https://p.dw.com/p/38EWq
Israel Benjamin Netanyahu und Avigdor Liberman in Tel Aviv
Hoto: Getty Images/L. Mizrahi

Ministan tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman mai tsattsauran ra'ayin kishin kasa ya soki lamirin yarjejeniyar wacce ya bayyana a matsayin yin saranda ga ta'addanci. Tuni ma ya sanar da ficewar jam'iyyarsa ta Isra'ila Beiteinou daga cikin kawancen masu mulkin, kana ya yi kira da a shirya zaben gaba da wa'adi na 'yan majalisar dokoki da ya kamata a shirya a watan Nuwamban 2019. 

Wannan murabus na nufin cewa a yanzu firaministan kasar ta Isra'ila na da karamin rinjaye ne na kuri'a dai tilo a majalisar dokokin kasar, lamarin da ya jefa rudani a game da makomar gwamnatinsa wacce aka kafa a shekara ta 2015 da kuma ake yi wa kallon mafi karfi a tarihin kasar ta Isra'ila.