1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Ministan harkokin waje ya yi murabus

Abdul-raheem Hassan
February 26, 2019

Ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif ya yi murabus ba zato ba tsammani ba tare da bayyana asalin dalilin daukar mataki ajiye aikin ba.

https://p.dw.com/p/3E6HX
Iran, Teheran: Außenminister Mohammed Dschawad Sarif verkündet Rücktritt
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Da yake sanar da matakin ta shafin Instagram Zarif ya nemi afuwar gwamnati da daukacin al'ummar kasar Iran kan matakinsa na rashin iya ci gaba da aiki a matsayin ministan harkokin wajen kasar. Ya kuma mika godiya ga ilahirin kasar da ma dukkannin jami'an gwamnati da suka ba shi hadin kai a yayin gudanar da aiki.

Ana danganta matakin ministan da matsin lambar da suke fuskanta daga Shugaba Hassan Rouhani kan yarjejeniyar soke makaman nukiliya, da sabbin takunkumin kasuwanci da kasar ke fuskanta daga kasashe kamar Amirka.

Murabus Javad Zarif bai karbu ba har sai ya samu amincewar Shugaba Hassan Rouhani, abin da masana siyasar kasar ke ganin da kamar wuya.