Minista shari′a ta Faransa ta yi marabus | Labarai | DW | 27.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Minista shari'a ta Faransa ta yi marabus

Ministan Christiane Taubira ta ajiye aiki ne saboda rashin amincewar da wani kudirin dokar wanda gwamnatin take shirin gabatar da shi a gaban majalisar dokokin.

Minitan shari'a ta ƙasar Faransa Christiane Taubira ta gabatar da takarda marabus ga shugaba Francois Hollande.Ministan ta ajiye aiki ne saboda rashin amincewar da wani ƙudirin dokar wanda gwamnatin take shirin gabatar da shi a gaban majalisar dokokin. Wanda zai soke takardar zaman ɗan ƙasa ga wanda aka samu da laifin yin aiyyukan ta'addanci

Marabus ɗin na ministan na zuwa ne a daidai lokacin da aka shirya yau majalisar dokokin Faransar za ta tattauna a kan wannan ƙudirin doka.Kuma tuni da shugaba Francois Hollande wanda ke da sabannin ra'ayi da ministar a kan wannan batu.Ya nada Jean Jacque Urvoas wani ɗan majalisar dokokin na jam'iyyar masu mulkin ta 'yan gurguzu a matsayin ministan shari'ar domin maye gurbin Christiane Taubira.