Michel Kafando zai jagoranci gwamnatin a Burkina Faso | Labarai | DW | 17.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Michel Kafando zai jagoranci gwamnatin a Burkina Faso

Tshohon ministan harkokin wajen na Burkina Faso dai ba zai shiga a dama da shi ba cikin fafutukar neman darewa mulkin kasa a zaben da za a yi a karshen badi.

Mahukunta a kasar sun bayyana sunan tsohon ministan harkokin kasashen waje Michel Kafando a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar. Jawabin hakan ya fito ne a yau Litinin a wani bangare na sake maida kasar bisa turbar demokradiyya, bayan wani takaitaccen lokaci na komawarta hannun mulkin soja.

Kafando dai zai jagoranci kasar ta Burkina Faso bayan wata mummunar zanga-zangar ranar 30 ga watan Oktoba, da ta tisa keyar gwamnatin Blaise Compaore bayan shekaru 27 yana mulki, inda Kanar Isaac Zida ya karbi jagorancin kasar .

Nan gaba ana sa ran Michel Kafando zai bayyana sunan Firaminista da zai kafa gwamnati mai mambobi 25. Sai dai ba zai shiga takaran shugaban kasa ba kamar yadda sojoji da shugabannin jam'iyyu da hadin gwiwar shugabannin jama'a suka cimma yarjejeniya, bayan kifar da gwamnatin Compaore.

Dama sun amince duk wanda zai rike gwamnatin kafin a gudanar da zabe, to dole a haramta masa shiga takara, domin gudun kada a sake yi musu irin dabarar da Balaise Compaore ya yi, inda ya yaudare 'yan kasar bayan juyin mulkin da ya yi wa Thomas Sankara. An dai shirya gudanar da zabe bayan shekara daya, inda za a sake kwaskwarima ga hukumomi da dama, kama daga kundin tsarin mulki har izuwa tsarin gudanar da zabe.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Usman Shehu Usman