1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or

Ramatu Garba Baba
November 30, 2021

An kamalla bikin bayar da kyautar Ballon d'or inda a karo na 7 a jere, Lionel Messi na kasar Ajentina mai taka leda a Kungiyar Paris St Germain ya lashe kyautar ta bana.

https://p.dw.com/p/43eKG
Frankreich Ballon d'Or 2021 Lionel Messi Sieger
Hoto: Franck Fife/AFP

Shahararren dan wasan da ya kafa sabon tarihi ta hanyar cin yawan kwallaye wa kungiyarsa fiye da wanda gwarzon kwallon kafar duniya Pele ya ci wa kungiyarsa, ya kasance a sahun gaba a manyan gasar Turai bayan da ya ci kwallaye akalla ashirin a kaka 13 a jere a nahiyar Turan.

A daya bangaren kuwa, Robert Lewandowski na kasar Poland kuma dan wasan Kungiyar Bayern Munich na Jamus, shi aka bai wa kyautar dan wasan tamola, wanda aka ce, ya kasance mai cin kwallon da babu kamarsa a tarihi a rukunin wata sabuwar kyautar da aka kirkira a bana.