Merkel ta yi kiran yin watsi da kyama a Jamus | Labarai | DW | 27.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yi kiran yin watsi da kyama a Jamus

Hukumomin Jamus sun bayyana bukatar ci gaba da yaki da kyama dai dai lokacin da kasar ke ranar tunawa da kisan kiyashin da 'yan Nazi suka yi wa Yahudawan a zamanin yakin duniya na biyu.

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta ce a ranar irin ta yau, zai fi dacewa a rika yin la'akari da rashin kyawun bambancin launin fata ko rashin imani, tana mai jaddada muhimmancin Jamusawa da ke da ra'ayin su yi watsi da hakan.

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, shi ma ya yi kiran a sauya tsarin sanar da mutane abubuwan da suka wakana lokacin kisan kiyashin da 'yan Nazi suka yi wa miliyoyin Yahudawa lokacin yakin na duniya.

A cewar Heiko Maas, zai fi kyau ne a yi amfani da bangarori masu muhimmanci ga jama'a a tarihin, maimakon wadanda ake karfafawa.