Merkel ta tattauna da DW kafin taron G7 | Labarai | DW | 06.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta tattauna da DW kafin taron G7

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce za su tattauna kan kasuwanci da ɗumamayar yanayi da kiwon lafiya da maganar yaƙi da talauci da kuma samar da tsaro.

Gabannin taron ƙasashe guda bakwai masu ƙarfin tattalin arzikin masana'antu a duniya wato G7 wanda za a soma a gobe Lahadi da Litinin a nan Jamus, Angela Merkel shugabar gwamnatin ta Jamus ta tattauna da DW a kan manufofin da taron ke shirin cimmawa, Wanda ya haɗa ƙasashen Faransa da Birtaniya da Japan da Canada da Italiya da Amirka da kuma Jamus ɗin mai masabkin baƙi,

Ta ce ''A wurina abIn da ke da mahimmanci a wannan ganawa da shugabannin ƙasashen guda bakwai shi ne mu canza yawu dangane da yadda za a iya shawo kan matsalolin da ke a gabanmu a cikin shekara mai zuwa, mu duba inda muke da saɓani ra'ayoyi da kuma inda bakinmu ya zo daya.''

An tsara taron zai taɓo batun kasuwanci da ɗumamayar yanayi da kiwon lafiya da maganar yaƙi da talauci da kuma samar da tsaro.