1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na ci gaba da ziyara a kasashen Afirka

August 30, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus za ta gana da shugaban Ghana a ci gaba da ziyarar da ta ke yi a wasu kasashen nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/342nG
Berlin, Ghanas Präsident Addo Dankwa bei Kanzlerin Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/B.von Jutrczenka

A wannan Alhamis ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, za ta gana da shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana a ci gaba da ziyarar da ta ke yi a wasu kasashen nahiyar Afirka.

A ranar Laraba ne Angela Merkel ta kasance a Senegal, a ziyarar kasashen da ta ke yi da nufin inganta huldar arziki da kuma kawo karshen kwararar bakin haure daga wasu kasashen na Afirka zuwa nahiyar Turai.

A gobe Juma'a ne kuwa shugabar gwamnatin ta Jamus za ta ziyarci Najeriya, inda za ta gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja fadar gwamnatin kasar, a kokarin da ta ke yi na kyautata alaka da kasashen na Afirka.