Merkel da Macron na halartar taron COP23 | Labarai | DW | 15.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel da Macron na halartar taron COP23

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da shugaban Faransa za su halarci taro kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da ke wakana a birnin Bonn.

A wannan Larabar ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron, ke gabatar da jawabai a taro kan maganta matsalar sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin Bonn.

Shugabannin biyu za kuma su hadu da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres, inda za su tattauna matsalolin yanayin da nahiyar Turai da kuma sauran sassa na duniya ke fuskanta.

Masu fafutikar kare muhalli a Jamus na kyautata fatan Angela Merkel, za ta tabo batun makamashin Kwal, wanda kasar Jamus ke samun wutar lantarkinta da kimanin kashi 40 cikin dari. Kwararru a fannin kimiyya dai sun ce da wuya ne a iya rage dumamar yanayi da mizanin digiri 2 na ma'aunin Celcius, kamar yadda kasashe suka bayyana a yarjejeniyar da suka cimma a birnin Paris shekaru biyun da suka gabata.