Menene sha′awar Faransa a kasar Mali? | Siyasa | DW | 17.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Menene sha'awar Faransa a kasar Mali?

A bayan dalilai na tsaro, Faransa tana da sha'awar tattalin arziki a yankin Afirka ta yamma, musamman kare hanyoyinta na samun sinadarin Uranium

Masana da masu lura da al'amuran yau da kullum, suna ci gaba da muhawara a game da dalilan da suka sanya Faransa a yanzu ta dauki matakin amfani da karfin soja kan yan tawayen da suka mamaye arewacin Mali, kuma suke barazanar karbe kudancin kasar. Shin Faransa din tana hakan ne saboda ceto kasar ta Mali da taimakonta ga komawa tafarkin democradiya, ko kuwa akwai wani buri da Faransa din ta sanya a gabanta: alal misali saboda neman dora hannunta kan albarkatun da yankin yake yake dasu?

Babu dai mai iya sanin tsawon lokacin da Faransa zata dauka tana amfani da karfin soja a Mali, saboda idan har ana bukatar hana kungiyoyin musulmi yan tawaye su fadada aiyukansu zuwa kudancinta, tilas ne a tsabtace yankin gaba daya, a kuma dauki matakin hana sake fadawarsa a hannun irin wadannan kungiyoyi nan gaba. Saboda haka ne kungiyar kare tsirarun kabilu ta kasa da kasa, tayi kira da a gabatar da wani tsarin da ya dace wanda kuma za'a iya aiwatar dashi. Ulrich Delius kakakin kungiyar kan nahiyar Afirka ya baiyana imanin cewar yan tawayen zasu koma amfani da dabarun da suka saba, wato su janye zuwa tsaunuka da duk wani kogo dake yankin, su kara daura damarar yaki.

Frankreich Hollande Algerien

Shugaban Faransa Francois Hollande

Gwamnatin Faransa tace batun batun tsaro shine kan gaba a manufofinta a Mali. Gwamnati a Paris tace babban dalilin kai hare-harenta shine tun da wuri, a hana yan tawayen na Afirka ta yamma su zama barazana ga nahiyar Turai. Faransa tana tsoron Mali tana iya zama maboya, kuma dandalin horad da yan ta'adda musulmi, idan har aka kai ga kafa kasa mai bin shari'ar musulunci a can, inji Katrin Sold, ta cibiyar al'amuran ketare a Berlin. Bugu da kari kuma, Faransa tana tsoron idan har bata dauki mataki a yanzu ba, ita kanta tana iya fuskantar hare-haren yan tarzoma a matsayin tsohuwar kasar da tayiwa Mali din mulkin mallaka. Tun shekara ta 2010 kungiyoyin musulmi suke rike da ma'aikatan kamfanin Faransa na AREVA, yayin da kungiyar al-Qaeda yanzu tayi barazanar kame wasu daga cikin Faransawa 5000 dake zaune a Mali.

A French army officer (R) talks to his Malian

Sojan Faransa a Mali

To sai dai kamar yadda Ulrich Delius ya nunar, Faransa ba batun tsaro kadai take sha'awarsa a yankin na Sahel ba. Ya zuwa wani dogon lokaci, kasar tana da sha'awar abin da zata samu na albarkatun kasa a yankin, musamman man fetur da Uranium, wanda ma kamfanin Faransa na AREVA tun shekara da shekaru yake aikin hako shi a makwabciyar kasar Nijer.

"Yace ba daidai bane idan shugaban Faransa, Francois Hollande a yan kwanakin nan yaci gaba da fadin cewar kasar sa tana wannan yaki ne ba tare da neman wata riba ko cimma wani buri ba. Babu shakka Faransa tana da sha'awar tattalin arziki a yankin , musamman bisa tabbatar da ganin ba'a sami katsewar sinadarin Uranium da take samu ba."

Duk da haka, Katrin Sold daga cibiyar al'amuran ketare a Berlin tace za'a dauki lokaci mai tsawo kafin Faransa taci gajiyar albarkatun kasa a Mali, saboda haka ne ake ganin shisshigin soja da Faransa din take yi yanzu yafi dangantaka da batun tsaro din a zahiri. A daya hannun, Ulrich Delius ya tunatar da hare-haren sojojin Faransa a Libya shekaru biyu da suka wuce inda yake cewa:

"A wannan lokaci, kasashe da dama sun baiyana sha'awarsu kan kasar ta Libya, musamman saboda arzikinta na man fetur, tun daga Jamusawa har ya zuwa ga Italiyawa da yan Austria. Faransa ta gudanar da al'amuran ciniki masu yawa da Libya, yayin da sauran kasashen suka fi sha'awar man fetur daga kasar. Amma a Mali al'amarin ba haka yake ba. Babu shakka Faransa tana da sha'awar abin dake gudana a Mali ne saboda makomar samun makamashin Faransa din ya dogara ne ga zaman lafiyar makwabciyar Mali, wato jamhuriyar Nijer."

Ko da shike Faransa tana iya fadawa zargin bullo da wani sabon salo na mulkin mallaka sakamakon matakin nata na soja a Mali, amma akalla a wannan karo, inji Alexander Stroh, na cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum mai suna GIGA, Faransa din ta tura sojojinne bisa dacewa da kudirin majalisar dinkin duniya na watan Disamba shekara ta 2012. Haka kuma, Faransa din ta amsa roko ne daga Mali, domin ta taimaka game da hana yan tawayen kan hanyar su ta mamaye kudancin kasar.

Mawallafi: Rachel Baig/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin