Menene cutar “Virus’’ na Na’ura mai kwakwalwa | Amsoshin takardunku | DW | 23.07.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Menene cutar “Virus’’ na Na’ura mai kwakwalwa

Bayanin yadda Na’urar kwamfuyuta take kamuwa da cutar “Virus’’

Cutar Virus ta na'ura maikwakwalwa

Cutar Virus ta na'ura maikwakwalwa

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawar mut a wannan makon ta fito daga hannun Malam Yahaya Sadiq daga Jihar Kano a Tarayyar Najeriya; Malamin cewa ya yi, Shin menene ake abinda ake kira da suna Virus Na Na’ura Mai kwakwalwa?Kuma yaya kwamfuta take kamuwa da wannan ciwo; kuma idan da hali a bani bayani kann yawan wannan ciwo.

Amsa: To mun dai mika wannan tambaya ga Injiniyan Na’ura maikwakwalwa, wato Malam Hashim Gumel, mamallakin shafinnan na yanar-gizo mai suna“gumel.com’’, Ga kuma tattaunawar da muka yi da shi , dangane da amsar wannan tambaya.

Bashir: Injiniya;Menene cutar Virus na Na’ura mai kwakwalwa?

Gumel: Malam Abba ita wannan cutar da akey kira da sunan virus, ta kasu fani daban daban, to a cikin mafiyan idan za’a dangana cutar virus sune guda uku.

1. Ita virus din kanta

2.Trojen horse wato Dokin Trojen

3.Warm Virus Annobar Tsutsa

Bashir: Menene Virus

Gumel: Wannan cutar annoba ta na’ura mai kwakwalwa mai suna virus,ko kuma muce cutar Sankara a hausance, wani dan guntun nau’i ne wanda yake manne kansa cikin nau’o’in dake cikin na’ura mai kwakwalwa,

kuma ita wannan cutar sankara tana lalata dukkan na’u’in, da kuma abinda ke cikin komputa, kamar gurin ajiya, da kundi, da takardun ku.

Kamar dai yadda muka san cutar annobar sankara ko kuma cutar daji ta Dan Adam, daga kan Agana , Sankarau, Gyanda da kuma HIV wato cuta mai karya garkuwar jiki,to ita ma wannan annobar takan hana na’ura bin ka’idar da tasaba lokacin da aka kunna ta, kai karshe ma dai takan sa kwamfuta ta mutu kurmus.

Wani abu daya dazan iya cewa agame da annobar na’ura maikwakwalwa shine, annobar computer bata yaduwa da Kanta, sai da taimakon Dan- Adam,

Bashir: To menene worm virus?Wato annobar tsutsa.

Gumel: Ita kuma wannan cutar da ake kira da sunnan Annobar tsutsa, an zaiyana ta ne da niyar ta kwaikwayi kanta daga cikin na’ura ya zuwa wata na’ura. kuma duk cikin na’urar da ta samu kanta, takan kwace ragamar mulkin na’urar ku, yadda zata iya aika kanta ya zuwa wasu na’urori batare da sanin mutum ba.

Babban hadarin wannan tsutsar annobar shine yadda take iya kwaikwayar kanta da kanta da dunbin yawa fiye da yadda mutum ya tsammata.

Ita wannan cuta tana yaduwa ne da kanta batare da wani ya taimaka mata ba, tana yin hakane ta hanyar aika kanta ya zuwa dukkan wanda suke cikin kudin adireshin dake cikin wasikar yanar gizo a cikin na’urarku mai kwakwalwa. Daga nan kuma zata sake maimaita wannan, daga na’urar wadanda suka samu wasikar da ta aika da kanta, kafin a fahimta ta zama ruwan dare gama duniya.

Ita wannan cutar bata bukatar amfani da wani nau’i ko kundi ta yadu cikin duniyar computer, to wanna zai iya ba wani dama daga wani nisan duniya ya kwace mulkin computer daga mai ita, ya kuma iya ‘barna ga computer ku.

Bashir: Me Nene cutar Trojan Horse virus?

Gumel: Dokin Trojen wanda akewa kirari da Lumbu-Lumbu wutar KayKayi, ita ma annoba ce, amma ta bambanta da sauran annobai ,domin ita wanna wani nau’i ne wanda aka zayyana domin wani aiki na gari, amma a hakikanin gaskiya domin barna aka yishi.

Ganin haka mutane sukan yadda su sa cikin Na’urar su, to maimakon amfaninta na gari sai ta lallaba ta Bude dukkan Kofofin da ke kulle, kuma ta tsaida dukkan rigakafin dake cikin Na’urar ku wanda kuka sa domin kare ciwon annoba,

Tana kuma karya Bangon karfin (firewall) da kuka sa, domin kare kanku daga miyagun mutane, domin kada su sami shiga cikin na’urar ku suyi barna.

Ita wannan cutar ana samuntane daga hanya ta gaskiya wadda baku zatun cuta daga hanyar.

Takan zo ta hanyar samun wasika wadda aka aiko maku da wani kundi ko nau’i wanda kuke zato mai amfani, amma sai ya kasance cuta ce aka aiko maku.

Kuma za a iya samun ta, ta hanyar janyo nau’i ko kuma program wato shiri , ta yanar gizo, ya zuwa na’urar ku wanda aka yi muka talla kyauta.

Sabo da haka yarda da janyowa wani nau’i na kyauta ta hanyar yanar gizo yana da hadari.

Bashir: Yaya Take yaduwa?

Gumel: Kamar yadda nayi bayani a baya, dukkan wadannan annobar computer sukan yadu ta hanyar taimakawa daga masu anfani da na’ura mai kwakwalwa,

Saboda haka idan kaga wasikar yanar gizo hade da wani kundi wanda ake kira da

suna file daga wanda baka tsammani wani abu makamancin haka ba, to kada ka

bude, sai ka kira shi wanda ya aiko maka kaji ku yana da masaniyar haka,

domin ita wannan cutar ta kan aika kanta da kanta ga dukkan wanda suke cikin

adereshin wasikar ka batare da sanin kaba.

Kuma mu guji amfani da fefan disk wanda ya fito daga abokin ka kokuma wanda baka aunashi ba,da abin rigakafin annoba, wanda yake a cikin na’urar ka.

Bashir: Ta yaya Mutum zai san cewa yana da cutur virus a na’urarsa

Gumel: A kwai Hanyoyi da dama wadanda zamu iya gane wa idan har na’urar mu ta kamu da ciwon annobar virus.

Da farko shine na’urar ku zata fara sansarafa da jan ciki, zaku ga a da tafi sauri wajen bude kundi ko shafi. Wani lokacin zaku ga bata sauraron dukkan umarnin da kuka bata, Zara rika kashe kanta da kuma kunna kanta lokacin da kake amfani da ita, a wani lokacin kuma ita wanna cutar zata lalata kudin, wanda ake kira file, mai mahimmancin amfani ga ita na’urar, sabodahaka lokacin da ka kashe ta, ka sake kunnawa sai taki aiki, kayi kayi ba yadda zaka yi sai mai gyara.

Bashir: Kot a yaya za’a iya Rage hatsarin kamuwa Cutar Virus ta na’ura maikwakwalwa.

Gumel: To babu wani abinda zai baka garanti dari-bisa-dari kan kariya daga wanna cuta,

amma zaka iya tsaftace na’urar ka bisa tabbatar da janyo makarrabe daga kamfanin makurosot wanda ake kira da Service Park , kuma mutum ya dasa maganin rigakafi wanda ake kira da anti-virus, kuma ku tabbatar da katangar karfen ku tana tsaye.

 • Kwanan wata 23.07.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvUn
 • Kwanan wata 23.07.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvUn