1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mdd zata dauki sabon mataki akan kasar Syria...

December 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvEb

Jakadan Amurka a Mdd, John Bolton yace yana cike da fatan cewa a sabuwar shekara majalisar zata dauki mataki na ladaftar da kasar Syria, bisa rashin cikakken hadin kai da basa bawa jami´an majalisar game da binciken rasuwar tsohon faraministan Lebanon, wato Rafik Hariri.

A can baya dai kwamitin sulhu na Mdd ya soki lamirin mahukuntan na Syria da gaza bawa kwamitin binciken hadin kann daya kamata game da binciken musabbabin tashin bom din daya halaka tsohon faraministan na Lebanon da wasu mutane sama da dozin daya.

A can baya dai mahukuntan na Syria sun shaidar da cewa a shirya suke su bayar da duk wani goyon bayan da ake bukata a game da wannan bincike.

Rahoton baya bayan nan dai da kwamitin binciken karkashin wani Bajamushe, wato Mehlis Detlav, ya mikawa Mdd ya tabbatar da cewa akwai sa hannun jami´ai gwamnati na Syria dana Lebanon a cikin bom din daya halaka Rafik Haririn.