MDD zata ci-gaba da taimakawa Kongo a aikin sake gina kasar | Labarai | DW | 27.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD zata ci-gaba da taimakawa Kongo a aikin sake gina kasar

A ziyararsa ta farko zuwa Afirka tun bayan darewa kan mukamin babban sakataren MDD, a yau Ban Ki Moon ya fadawa al´umar JDK cewar suna iya dogaro ga taimakon MDD a aikin sake gina kasar. A jawabin da yayiwa sabuwar majalisar dokokin Kongo, Mista Ban kuma yayi kokarin kawad da fargabar da ake yi cewar MDD na shirin rage yawan sojojin kiyaye zaman lafiya a Kongo bayan zaben da aka gudanar kasar a bara. A cikin wata mai zuwa kwamitin sulhu zai kada kuri´a akan sabunta wa´adin tawagar MDD a Kongo, inda membobin kwamitin zasu yanke shawara akan ci-gaba da zaman sojojin su dubu 17. Ban zai kuma kai ziyara a janhuriyar Kongo da kuma Habasha a wannan rangadi nasa a Afirka.