MDD za ta hukunta Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 05.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD za ta hukunta Koriya ta Arewa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin amincewa da wani kudirin wanda zai haramta wa Koriya ta Arewa taba kudaden da suke shigo ma ta sama da biliyan daya.

Matakin dai na da nufin  tilasta wa Koriya da ta ci tuwon fashi a game da shirinta na nukiliya wanda ake ta yi takkadama a kan sa tun bayan da ta jarraba manyan makamai masu linzami masu cin dogon zango da ka iya zuwa daga nahiya zuwa nahiya. Kudirin wanda zai shafi kudaden da kasar ta ke samu na shiga ta hanyar kwal da ta kan fitarwa waje da kifi da kayan marmari na iya gamuwa da cikas na kasashen Rasha da China.