MDD: Za mu tallafa wa kasashen Sahel | Labarai | DW | 23.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Za mu tallafa wa kasashen Sahel

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi alkawarin tallafa wa kasashen yankin Sahel wajen ganin sun kaiga murkushe ta'addanci da ke durkusar da harkoki a yankin.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jakadan tsaron majalisar, Tekeda Alemu, wanda ya jagoranci wata tawagar da ta hada wasu jakadun Faransa da Italiya gami da wasu jiga-jigan su 15, inda suka tabbatar da hakan ne a karshen ziyarar kwanaki 5 da suka kai wa yankin.

Dama dai kasashen na yankin Sahel, wadanda suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritaniya da kuma Jamhuriyar Nijar na daf da kammala shirye-shiryen kaddamar da runduna ta musamman a karshen wannan wata na Oktoba, don fuskantar mayakan na tarzoma.

A 'yan watannin nan ma dai an sami tabarbarewar lamuran tsaro a yankin, musamman ma a tsakiyar kasar Mali, lamarin da ya tsananta bukatar zafafa shirin sintiri kan 'yan tarzomar.