MDD: ′Yan hijira sun karu a duniya | Labarai | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: 'Yan hijira sun karu a duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce masu zaman hijira a duniya sun yi matukar karuwa a shekaru takwas din da suka gabata, daga mutum miliyan 42 zuwa mutum miliyan 66.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce masu zaman hijira a duniya sun yi matukar karuwa a shekaru takwas din da suka gabata, daga mutum miliyan 42 zuwa mutum miliyan 66. A cewar hukumar raguwar kokarin al'umar duniya na rage ko kuma sasanta rigingimu ne ke zama musabbabin ta'azzarar wannan lamari.

Wani babban jami'i a hukumar Filippo Grandi, shi ne ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya hakan a birnin New Yorka na Amirka. Kuma kasashen Syria da Iraki kadai sun kwashi kaso mafi yawa na wadanda suka bar muhallansu a duniyar yau. Na baya-bayan nan kuwa su ne wasu musulmi marasa rinjaye 'yan Rohingya na kasar Bama su dubu 500 da rikici ya raba da sukuni inda a halin yanzu suke fakewa a kasar Bagaladash.