1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi kashedi kan 'yan Rohingya

November 11, 2017

Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres ta ce wajibi a dakatar da cin zarafin Musulmi marasa rinjaye 'yan kasar Bama, a kuma samar masu yanayin komawa wurarensu.

https://p.dw.com/p/2nST7
UN Symbolbild Flagge
Hoto: Imago/imagebroker/E. Börnsch

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres ya ce wajibi ne a dakatar da cin zarafin Musulmi marasa rinjaye 'yan kasar Bama, a kuma samar da yanayin da za su iya komawa yankinsu. Mr. Gutterres ya kuma ce Majalisar ta bukaci da a bude duk wasu hanyoyin kai kayan tallafi a dukkanin yankunanda ke arewacin jihar Rakhine. Sama da mutum dubu 600 ne ke zaune a jihar ta Rakhine a baya, kafin su tsere zuwa kasar Bangaladash sakamakon barkewar rigima tsakaninsu da sojojin Myanmar.

Jagoran na MDD, zai kuma gana da wasu shugabannin kasashen Turai da na kudu maso gabashin Asiya domin duba matsalolin musulmin na Rohingya.

Jagorar Myanmar Aung San Suu Kyi, wadda ta sha suka daga kasashen duniya kan cin zarafin al'umar ta Rohingya, za ta kasance a zaman da zai yi nazarcin halin da Musulmin na Bama suka shiga, a taron da za su yi a kasar Phillipines.