1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi gargadin aukuwar yunwa a Gaza

Abdullahi Tanko Bala
December 22, 2023

A'ummar Gaza na fuskantar hadarin bala'in yunwa sakamakon yakin da ke ci gaba da gudana tsakanin Israila da Hamas a cewar Majalisar Dinkin Duniya

https://p.dw.com/p/4aUo1
Falasdinawa na fafutukar neman abinci a Rafah
Hoto: Fatima Shbair/AP Photo/picture alliance

Majalisar Dinkin duniyar ta sanar da hakan ne gabanin kuri'ar da ake sa rai  kwamitin sulhu zai kada a wannan Juma'ar kan kudirin bunkasa taimakon jinkai ga yankin Falasdinawa, amma kudirin bai hada da kiran tsagaita wuta ba.

Jami'an diflomasiyya dai na kokarin gabatar da sabon yunkuri na neman tsagaita wuta a rikicin da ya samo asali daga harin da Hamas ta kai wa Israila a watan Oktoba.

Karin Bayani: Gaza: Ana ci gaba da kiran tsagaita wuta

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutanen Gaza miliyan daya da dubu dari tara sun tagaiyara daga cikin al'umar yankin miliyan biyu da dubu dari hudu.

Israila ta ci gaba da  tsanata hare hare a Gaza yayin da Hamas ta harba makamin roka zuwa cikin Tel Aviv.

A kalla mutane 20,000 suka rasa rayukansu a Gaza tun bayan barkewar yakin a cewar ma'aikatar lafiya ta hukumar  Falasdinawa.