MDD ta yi alkwari ga rundunar G5 Sahel | Labarai | DW | 30.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta yi alkwari ga rundunar G5 Sahel

Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin samar da dala miliyan 60 don kafa runduna ta musamman don yaki da ta'addanci a kasashen yankin Sahel.

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ne ya sanar da alkawarin kudaden yayin da kwamitin sulhun MDD ke zaman duba hanyoyin taimaka wa kasashen yankin na Sahel da ke shirin samar da runduna ta musamman ta tsaro. Sai dai a share guda, majalisar ta yi watsi da bukatar shugabannin nahiyar Afirka da Faransa da suka bukaci hannun majalisar dumu-dumu.

Jakadiyar Amirka a MDD Nikki Haley, ta ce lallai ne kasashen yankin na Sahel su kasance masu daukar nauyin wannan runduna. Haka nan ma ta yi watsi da bukatar rundunar samar da zaman lafiya ta MDD wato MUNUSMA ta shige cikin rundunar ta G5 Sahel.